Kungiyar likitocin dai ta shiga yajin aikin ne da ta kira na gargadi a ranar Laraba 17 zuwa 22 ga watan mayu 2023.
Daga cikin bukatun kungiyar likitocin sun hada da karancin ma’aikatan kiwon lafiya sakamakon fita waje da su ke yi neman aiki mai gwabi a inda hakan ke haddasa rashin kyakyawar fahimta tsakanin masu neman lafiya da kuma su ma’aikan, lokacin tsarin maye gurbin ma’aikaci, da kuma janye kudirin hana likitoci fita kasashen waje har sai sun yi aikin shekara biyar a kasar, karin albashi zuwa kashi 200 ciki dari na albashinsu, da kuma alawus-alawus da dai sauransu.
Ko wani mataki kungiyar likitocin za ta dauka bayan cikar wa’adin kwanaki biyar din? Dr. Godiya Ishaya shi ne tsohon Shugaban kungiyar ta NARD kuma ya na magana ne da yawun shugaban kungiyar na yanzu Dr. Orji Emeka Innocent.
A martanin gwamnatin Najeriya game da yajin aikin na likitoci, ta yi barazanar maye gurbin likitocin da ma’aikata na wucin gadi ta bakin Ministan kwadago Chris Ngige a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Chennels kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Da ya ke magana game da batun sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC Kwamred Nasir Kabir ya ce maganar ministan na kwadago ba ta da tushe ballantana makama.
Mai sharhi kan lamuran yau da kullum Aliyu Shamaki ya ce daukan wannan matakin na nuna gazawar gwamnati wajen biyan hakkin yan kasar.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar: