Masana da kwararru kan aikin jarida a Amurka da na kasashe masu tasowa irin su Najeriya na ci gaba da yin tsokaci dangane da irin rawar da kafafen labarai na kasashen yamma ke takawa na bada rahotannin da suka shafi Afirka.
Batun ta’addancin Boko Haram a Najeriya shine ya mamaye taron da aka gudanar a jami’ar California, kan yaki da ta’addanci da ‘yan jaridu daga kasashen duniya suka halarta.
Bisa ga wasikar da hukumar SSS ta rubutawa Majalisar Dattawa ya sa majalisar ta ki amincewa Ibrahim Magu kujerar shugabancin hukumar EFCC a karo na biyu
Gwamantin Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da su dakatar da bulaguron da suke shirin yi zuwa Amurka, har sai an fahimci inda manufofin shugaba Donald Trump kan baki ya sa gaba.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta da hadin gwiwar jami’an leken asiri na DSS sun cafke wasu ‘yan Boko Haram ‘yan kasar Chadi a jihar Gombe.
Ana gudanar da baje-kolin wasu kayayyakin yaki da wasu injiniyoyin sojin Najeriya suka kera a babbar barikin soja ta Mambilla dake Abuja.
Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa sojojin saman kasar sun kai farmaki wasu kauyuka a jihar Borno bisa kuskure, inda aka rasa rayuka wasu kuma suka raunata.
Hedikwatar sojojin Najeriya tace dakarun kasar sun ‘kara kubutar da wata ‘dalibar makarantar sakandare ta garin Chibok daga hannun mayakan Boko Haram.
Masana na gargadin yiwuwar samun yakin sari-ka-noke daga mayakan Boko Haram biyon bayan fatattakarsu da rundunar sojan Najeriya tace ta yi daga sansaninsu na ‘karshe a dajin Sambisa.
Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce rundunar kai daukin gaggawa dake karkashin ofishin Sifeto Janal na ‘yan sandan kasar ta afkawa gungun wasu masu sace mutane da suka dade suna addabar al’ummar yankin Niger Delta.
Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya fitar da sanarwa inda ya nuna rashin jin dadi dangane da yadda aka kashe yan Shi’a a jihar Kano.
Kimanin Alhazai miliyan Biyu ne sukayi tsayuwan Arfa a wajen birnin makka, a matsayin wani babban ginshikin aikin hajji da musulmi ke gudanarwa duk shekara.
Dazu dazunnan wata babbar kotun Tarayya dake Abuja ta soke zaben gwamnan jihar Abia.
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emifiele, yace an dauki matakin barin Naira ta samawa kanta daraja gwargwadon yadda kasuwa ta kaya ne soboda hakan ka iya sawa ta kara daraja.