Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Nemi A Yi Taka Tsan-tsan Game Da Rikicin Yan Shi’a A Najeriya


Yan kungiyar Shi'a a Kano
Yan kungiyar Shi'a a Kano

Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya fitar da sanarwa inda ya nuna rashin jin dadi dangane da yadda aka kashe yan Shi’a a jihar Kano.

Cikin sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya aikawa sashin Hausa na Muryar Amurka mai dauke da sa hanun John Kirby, Amurkan tace ta damu matuka dangane da yadda yan sanda sukai amfani da karfin da ya wuce kima wajen tunkarar ‘yan Shi’ar.

Amurka ta ce yan Shi'a kamar sauran ‘yan Najeriya, suma na da yancin yin addininsu kamar yadda suka fahimta ciki har da tattaki matukar zasu yi shi cikin lumana, kuma dole ne Najeriya ta basu kariya, yayin da suma yan Shi’ar inji Amurka dole ne su bi dokar kasa.

Tuni dai sufeto janar na ‘yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris, yayin da yake magana kan rikicin na Kano yace mutane su gane cewa, inda yancin wani ya kare nan na wani ya soma, kuma kowane dan Najeriya nada hakkin da dole a kare mai.

Rundunar yan Sandan Najeriya dai ta zargi yan Shi’ar a kano da laifin afkawa jami’anta, zargin da yan Shi’ar suka musanta. Mallam Shu'aibu Ahmed na bangaren kungiyar ‘yan Shi’a, yace kungiyar na gudanar da harkar musulunci a Najeriya kusan shekaru Arba’in kenan wanda ba a taba samunsu da laifin tada hankaliba.

Tuni kuma masana irin su Dakta Abubakar Umar Kari, na Jami’ar Abuja sukayi gargadin cewa dole ayi taka tsantsan kan wannan rikici dake yawan faruwa tsakanin jami’an tsaron Najeriya da yan kungiyar Shi'a, kasancewar idan har ba a yi a hankali ba rikici kan iya ruruwa ya kuma addabi kowa a kasar. Dakta Kari, ya kuma ce kamata yayi rikicin Boko Haram ya zama darasi ga dukkan bangarorin biyu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG