Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Sojoji Sun Kai Hari Kan ‘yan Gudun Hijra Bisa Kuskure


Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa sojojin saman kasar sun kai farmaki wasu kauyuka a jihar Borno bisa kuskure, inda aka rasa rayuka wasu kuma suka raunata.

Lokacin da wakilin Muryar Amurka ya isa Hedikwatar tsaron Najeriya, ya tarar da wasu manyan kwamandojin sojin kasar suna wani taro na gaggawa.

Kakakin hedikwatar tsaron Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar, ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya ce kuskure ne aka samu.

Ya ce sojojin sun sami labarin cewa akwai ‘yan Boko Haram anan wasu kauyuka a Rann, hakan ya sa sojoji suka kai harin domin samun kubutar da mutanen ‘kauyen daga hannun ‘yan ta’addan.

Haka kuma an kara samun irin wannan kuskuren a wani kauye na karamar hukumar Kala Balge dake yankin Maiduguri a jihar Borno.

Sai dai har yanzu rundunar sojan ba ta fitar da rahotan ko mutane nawa ne suka rasa rayukansu a dalilin wannan hari da sojojin Najeriyan suka kai bisa kuskure ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG