Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Tsaro Sunyi Gargadi Kan Harin Sari-Ka-Noke


Masana na gargadin yiwuwar samun yakin sari-ka-noke daga mayakan Boko Haram biyon bayan fatattakarsu da rundunar sojan Najeriya tace ta yi daga sansaninsu na ‘karshe a dajin Sambisa.

Biyo bayan kwace dajin Sambisa daga hannun mayakan Boko Haram da dakarun Najeriya suka yi, masana tsaro na kiran da ayi taka tsan-tsan ganin yadda ‘yan Boko Haram din suka warwasu cikin jama’a garuruwa.

Kwararre kan yaki da ta’addanci Manjo Janal Yakubu mai Ritaya, yace ganin yadda har yanzu ba a san inda shugabansu yake ba, hakan ya zamanto tamkar an kashe maciji ba a sare mishi kai ba. yayi kuma kira ga shugabanni da al’umma da a bude ido a rika kula.

Shi kuma tsahon gwamnan mulkin soja a jahar Kano, Kanal Aminu Isa Kwantagora, cewa yayi dole ne yanzu kowa ya tashi tsaye ya lura, kasancewar yanzu barnar zata iya fin muni domin mutane basu san da wa suke zaune ba. ya kuma yi kira ga duk ‘yan Najeriya da cewa kowa ya zama sojan kansa yanzu.

Kwararre kan shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, Baba Yola Mohammadu Tango, yace ko da yake za a iya cewa yakin dajin Sambisa ya kare amma akwai sauran Rina a Kaba, saboda warwasuwar mayakan cikin al’umma. Yace abin yi yanzu shine rundunar soja ta aika da jami’an leken asirin ta zuwa kauyukan dake yankin domin nado bayanai.

Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG