Alhazan da suka fito daga kasashe daban daban na duniya tunda farko sun shafe yini daya a Muna shima dake wajen birnin na makka kafin daga bisani a debesu cikin manyan motocin safa safa zuwa filin na Arfa.
Wakilin sashin Hausa na muryar Amurka Hassan maina Kaina da shima ke cikin Alhazan yace mahukuntan daular saudiyya sun jibge dubban ‘yan Sandan kwantar da tarzoma don samar da cikakkiyar tsaro ga Alhazan, yayin da jirage masu saukar Ungulu na jami'an tsaron ke ta shawagi a kan sansanonin Alhazan.
Tun da yammacin jiya ne aka kwashe Alhazan daga Muna zuwa Muzdalifa inda nanma suke gudanar da wani bangare na aikin Hajjin.
In an jima kadanne kuma shugaban Hukumar Alhazan Najeriya Barrister Abdullahi Moukhtar Mohammed, zai yi taro da manema labaru dangane da shi aikin Hajjin.
Tuni Amirul Hajjin Alhazan Najeriya mai martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya nuna gamsuwa da yadda aikin hajjin ke tafiya ya zuwa yanzu.