Masanan dai sun ce matakin aikata barna da ya dabaibaye zanga-zangar da aka fara cikin lumana a ranar 1 ga watan Agustan da ya rikide zuwa wani abu na daban daga yini na biyu babban abun damuwa ne matuka, kuma dole ne dukkan masu ruwa da tsaki daga matakin tarayya zuwa kasa su dauki matakan da suka dace nan take don gudun abun da ka je ya dawo.
Tuni dai aka fara neman amsan tambayar ko kwalliya ta biya kudin sabulu ga manufar masu zanga-zangar ganin irin barnar da aka tafka kama daga asarar rayuka da dukiyoyi, baya ga cewa Shugaba Bola Tinubu a jawabin sa da ya yi wa 'yan kasa na ranar lahadi bai tabo muhimmman bukatun da masu zanga-zangar suka gabata ba gabanin fara zangazangar, shi ne daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, dan gwagwarmaya kuma lauya, Kwamared Deji Adeyanju ya ce an sami nasara kuma zanga-zangar ta yi tasiri.
A yayin da ake ci gaba da baiwa gwamnatin Najeriya shawarwari a kan mafita mai dorewa ga yanayin da ake ciki, shugaban jam’iyyar adawa ta SDP a matakin kasa Alhaji Shehu Musa Gabam, ya ce abun da ya kamata a yi a cikin lokaci guda al’umma su ji dadi, gwamnati bata yi ba, yana mai cewa, Najeriyar da Shugaba Tinubu ya sani a lokacin da ya karbi mulki, ba Najeriyar yau ba ce saboda yunwa, talauci da kuma rashin tsaro.
Shi ma masanin tsaro kuma tsohon babban dogarin marigayi shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa, duk gwamnatin da bata damu ta kula da wadanda suke cikin talauci a kasa ba, wata rana zata zo talakawan zasu cinye masu kudin, yana mai kira ga shugabannin kasa su tallafa a sami mafita daga cikin kangin da aka shiga.
Wasu masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum dai sun jadada cewa, dole ne gwamnatin Najeriya ta sake nazari kan manufofin ta da suka kai ga yanayin tsananin tsadar rayuwa da aka shiga musamman ganin cewa bayan kwashe tsawon shekara da fara aiwatar da manufofin, miliyoyin talakawa ba sa iya cin abinci sau daya a rana.
Alkaluman sun yi nuni da cewa, yankin arewacin Najeriya ne barnar da aka yi a zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa a kasar ya fi shafa musamman ganin rayukan da suka salwanta da dukiyoyin da aka lalata.
daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar wannan zanga-zanga, akwai wani yaro mai suna Isma’il Muhammad da wani faifan bidiyo ya yi nuni da cewa sojoji suka kashe shi a yayin aiwatar da dokar hana zirga-zirga a birnin zariya na jihar Kaduna da iyayenshi ke neman a bi musu kadun zalincin da aka yi musu.
Shelkwatar rundunar sojin Najeriya dai ta nuna alhininta a kan lamarin da ya afku a Zaria inda ta mika sakon jaje ga iyayen yaron yayinda kuma ta kama sojan da ake zargi da kashe matashin, yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike don daukan matakin da ya dace.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna