Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofar Mu A Bude Take Domin Tattaunawa Da Yin Sulhu Ga Masu Zanga-Zanga - Bola Tinubu


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci wadanda suka shirya zanga-zangar neman a kawo karshen tsadar rayuwa a kasa da su dakatar da duk wata zanga-zanga, domin kuwa kofar gwamnati a bude take a tattaunawa a kuma yi sulhu a samo hanyoyin kawo sauki a yanayin matsin da ‘yan kasa ke ciki a yanzu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin sa na farko ga al’ummar kasa tun bayan da masu zanga-zanga su ka fantsama kan titunan sassan kasar daban-daban a ranar 1 ga watan Agustan nan da muke ciki, wanda ya zo a yini na hudu da masu zanga-zangar su ka haye kan tituna, domin neman gwamnati ta biya musu bukatu, wanda jigo a ciki shi ne dawo da tallafin man fetur.

A cewar shugaba Tinubu, a bude kofar tattaunawa da yin sulhu ga ‘ya kasa take don samo mafita mai dorewa a cikin yanayin da ake ciki, kuma gwamnatinsa ba za ta saka ido ta bar wasu tsirarun mutane, masu boyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza Najeriya ba.

Yana mai yin kira ga wadanda suka shirya wannan zanga-zanga da masu yin ta umarnin su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da bude kofar tattaunawa da sulhu, kasancewar a matsayin shi na shugaba, wajibi ne a kan sa ya tabbatar da doka, oda da zaman lafiya ganin irin barnar da aka tafka a yayin zanga-zangar, inda aka sami asarar rayuka da dukiyoyi a wasu jihohi kamar Kano, Borno, Jigawa, Kaduna da dai sauransu.

Muhimman Abubuwa Da Jawabin Shugaba Tinubu Ya Kunsa

  1. Gwamnatinsa ba zata bar wasu tsirarun mutane su tada kayar baya ba sakamakon irin barnar da aka tafka a cikin kwanakin da aka fara zanga-zangar lumana da ta rikide zuwa wani abun na daban ba.
  2. Barnata kadarorin kasa babu abin da zai haifar sai mayar da Najeriya baya a matsayinta na al'umma, domin kuwa da dan abin da kasar ke da shi a matsayin arziki za a sake amfani wajen sake gina abin da aka lalata.
  3. Bai kamata a ci gaba da amfani da zubar da jini da tashin hankali da barna a matsayin hanyar neman biyan bukatu daga gwamna a bangaren ‘yan kasa ba.
  4. Najeriya na bukatar dukkan ‘yan kasa baki daya su hada kai ba tare da la'akari da bambancin shekaru, jam'iyya, kabila, addini, ko rarrabuwar kawuna ba, wajen gyara makomarta a matsayin kasa, ya na yin kira ga wadanda suka yi amfani da wannan yanayi da bai dace ba don yin barazana ga kowane bangare na kasar nan su daina, kuma muddin basu yi hakan ba doka za ta hau kan su saboda sabuwar Najeriyar da gwamnatinsa ke rajin ginawa, bata tanadi wani muhalli wa kabilanci ko barazana ga wani ba, yana mai kara da cewa tsarin dimokuradiyyar da kasar ke kai zai ci gaba ne kawai idan aka mutunta hakkin kowane dan Najeriya da tsarin mulki ya ba shi.
  5. Shugaban ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su yi amfani da hanyar da ta dace wajen ci gaba da tabbatar da doka da oda tare da bayar da cikakken tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, inda ya ce kudirinsa shi ne samar da kasa mai adalci da wadata, inda kowane mutum zai ci moriyar zaman lafiya, ’yanci, da rayuwa mai ma’ana da shugabanci nagari, bisa turbar gaskiya da rikon amanar al’ummar Najeriya.
  6. Tinubu ya kuma tabbatar da cewa Najeriya ta kai matsayin da ba zata iya ci gaba da yin amfani da hanyoyin magance matsaloli na wucin-gadi ba, domin magance matsalolin da suka dade suna ci wa al’umma tuwo a kwarya da kokarin ceton goben ‘yan kasar, kuma ba shi da zabin da ya wuce ya tsaya a kan matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kudaden waje da yawa wadanda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin kasar da ci gabanta.
  7. A cikin watanni 14 da suka gabata, gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen sake gina ginshikin tattalin arzikin Najeriya da zai ciyar da yau da goben ‘yan kasa gaba cikin wadata, misali, a bangaren kudaden-shiga kadai, an sami jimillar ya rubanya ninki biyu, inda ya kai sama da Naira tiriliyan 9.1 a rabin farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da rabin farkon shekarar 2023.
  8. Najeriya ta baro lokacin da kasar ke kashe kaso 97 cikin 100 na duk kudaden shigar da take samu wajen biyan bashi, a yanzu kaso 68 cikin 100 ne ke tafiya a biyan bashi, kuma wannan nasarar an same ta ne cikin watanni 13 kacal, in ji shugaba Tinubun.
  9. A cewarsa, gwamnatin da yake jagoranta ta kaddamar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin kasar, kuma ta na ci gaba da kammala ayyukan da ta gada da ke da mahimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar, wadanda su ka hada da samar da manyan hanyoyi, gadoji, layin dogo, wutar lantarki, matatun mai da iskar gas da dai sauransu. Misali, idan aka duba ayyukan babbar hanyar Legas zuwa Calabar da babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry za'a ga cewa za su bude wa jihohi 16 hanyoyin huldar ci gaban tattalin arzikin junansu, da samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki ta hanyar kasuwanci, yawon bude ido da musayar al’adu.
  10. Masana'antar man fetur da iskar gas din Najeriya da ke durkushewa a baya ta kama hanyar sake farfadowa, sakamakon sauye-sauyen da shi Tinubun ya sanar a watan Mayun shekarar 2024, don magance gibin da ke cikin dokar masana'antar man fetur wanda ya yi sanadiyar kara yawan man da kasar ke hakowa zuwa ganga miliyan 1.61 a kowace rana a watan da ya gabata, kuma kadarorin kasa na iskar gas na samun kulawar da ya kamata, in ji Tinubu.
  11. A cewar shugaba Tinubu, gwamnatin da yake jagoranta ta kafa cibiyoyin juya ababen hawa daga masu amfani da man fetur zuwa iskar gas a fadin kasar nan, tare da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, yana mai cewa sun yi imanin cewa wannan shirin na CNG zai rage farashin sufuri da kusan kashi 60 cikin 100 kuma zai taimaka a kokarin gwamnnati na dakile hauhawar farashin kayayyaki.
  12. Gwamnatin Tinubu ta kuma bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga dalibai mai suna NELFUND, inda a yanzu ta saki kudi da ya kai Naira biliyan 45.6 ga dalibai, sai kafa hukumar bayar da Lamuni ga masu bukata da aka zuba wa kimanin Naira Biliyan 200, sa’annan ta samar da zunzurutun kudade har dala miliyan 620 a ƙarƙashin shirin Digital and Creative Enterprises (IDICE) don ƙarfafa matasan kasa.
  13. Sai kuma shirin Gwarazan-Ƙwararru mai taken (SUPA); da Cibiyar Nazarin Matasa ta Najeriya (NIYA); ga kuma Shirin Zakulo Hazikan Matasa (NATEP), ware lamuni na kimanin Naira milyan daya ga kowanne mutum daya daga masu kananan sana`o`i har dubu 75 da za a fara rabawa daga wannan watan da dai sauransu a cikin tsare-tsaren kawo ci gaba da gwamnatinsa ta tanada wa `yan Najeriya, in ji shugaba Tinubu.

A karshe dai, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan kasa da cewa kada su bari wasu su ba da labarin kanzon-kurege na cewa gwamnatinsa ba ta damu da su ba, yana mai cewa su ba shi dama a yi aiki tare don gina kyakkyawar makoma ga kasar.

Ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, da doka da oda a kasar Najeriya a bisa la`akari da yarjejeniyoyin kare hakkin dan Adam da kasar ta sha rattaba hannu a kai kuma tsaron rayuka, lafiya da dukiyoyin dukkan 'yan Najeriya su ne abu mafi muhimmanci ga gwamnatinsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG