Majiyoyi daga kauyen da ke cikin karamar hukumar mulkin Goronyo sun ce maharan masu yawan gaske da ba'a iya tantance adadinsu ba sun kai hari a kasuwa a cikin daren ranar Lahadi inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labari dai ba’a iya tantance adadin wadanda suka rasa ransu yayin harin ba.
Wannan ne karo na uku cikin makwanni biyu da 'yan bindiga ke kai hare-hare a kasuwar kauye a jihar ta Sakkwato lamarin da wasu masana ke alakantawa da arcewar da wasu gungun yan bindiga suka yi daga dazukan jihar Zamfara bayan luguden wuta da sojojji su ka yi mu su, inda wasunsu suka yi kaura zuwa jihar ta Sakkwato.
Idan ana iya tunawa, a makon farkon wannan watan nan wasu mahara da ba’a san ko su wanene ba sun kashe mutane 20 a kasuwar Unguwar Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwaton.
A makwanni da suka wuce sojoji sun kaddamar da samame ta jirgin yakin sojin saman Najeriya a kan sansanonin 'yan bindiga a jihar Zamfara dake makwabtaka da jihar Sakkwato baya ga matakin da hukumomi suka dauka na rufe aiyukan sadarwa don katse sadarwa tsakanin kungiyoyin yan bindigar da ke da mazauni a cikin dazukan Zamfarar.
A baya-bayan nan rahotanni daga jihar Zamfara sun bayana cewa ’yan bindiga da ke tserewa samamen na soji a jihar sun kafa sansani a gundumar Sabon Birni daga inda suke kai hari kan kauyukan jihar Sakkwato.
Idan ana iya tunawa kuma, a cikin watan Satumban da ya gabata an kashe jami’an tsaron Najeriya kimanin 17 a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a sansaninsu da ke kauyen Dama na karamar hukumar Sabon Birni wanda sojoji suka zargi mayakan Jihadi masu alaka da kungiyar IS da aikatawa.
Masanin tsaro Kabir Adamu, ya sha nanata cewa kamata yayi gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi su duba lamarin tare da daukar matakin soji na bai daya a dukkannin jihohin arewa maso yamma dake fuskantar hare-hare yan bindiga, la’akari da yadda matakin da aka dauka a jihar Zamfara ya ba wa wasu batagari damar tserewa zuwa wasu jihohin makwabta.