Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'ar Zamfara Sun Gudanar Da Addu’ar Neman Zaman Lafiya


Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)

Wasu mazauna jihar Zamfara da suka kunshi kabilu daban-daban sun hada kai guri daya suka gudanar da addu’ar neman dauki kan matsalar tsaro da ke kara kamari a jihar.

Masu addu'ar wadanda akasari ma 'yan asalin jihar ta Zamfara ba ne sun kuma bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da isassun kayan aiki ga jami'an tsaro da ke yaki da 'yan fashi da sauran masu aikata muggan laifuka a jihar.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci zaman addu’ar sun bayyana cewa a gomman shekaru da suka kwashe suna zama a jihar ta Zamfara, ba su taba fuskantar matsalar rashin tsaro kamar na wannan lokacin ba.

Akan haka suka ce ya zame mu su wajibi su yi addau’ar neman zaman lafiya a inda suke rayuwa da ma dukkan Najeriya baki daya.

Hakan dai na zuwa ne a yayin ake fuskantan jerin hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, wanda na baya-bayan nan shi ne sace daliban makarantar sakandaren gwamnati da ke kaya a karamar hukumar Maradun su 73.

Wasu majiyoyi daga kauyen Kaya sun bayyana cewa maharan masu yawan gaske sun kutsa cikin makarantar ne a ranar 1 ga watan Satumba kuma suka yi awun gaba da daliban zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Sace daliban na Kaya shi ne hari na uku da aka kai kan makarantu a jihar Zamfara idan aka hada da na Jangebe da Bakura a cikin wannan shekara daya kawai.

Yawan hare-haren baya-bayan nan ya sa gwamnati ta dauki tsauraran matakan yaki da 'yan ta da kayar baya a jihar kamar rufe kasuwanni da ayukan sadarwa.

Bayan daukar matakan ne kuma rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da wani shirin yaki da 'yan bindigar a jihar, lamarin da 'yan Najeriya da dama suka yaba da shi, tare da fatar zai kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar ta Zamfara da ma makwabtan jihohi.

To sai dai kwanaki kalilan bayan aikin na soji, da kuma bude kafofin sadarwa, al'ummar jihar, musamman a yankin kananan hukumomin mulkin Shinkafi, Kaura Namoda, Zurmi, da Maradun, sun bayyana cewa ayukan 'yan bindigar sun dawo kamar da, ko ma fiye da yadda suke a da.

Lamarin ya kuma kara yaduwa zuwa makwabtan jihohi, musamman gabashin jihar Sokoto, inda rahotanni ke bayyana cewa ana samun hare-haren 'yan bindigar kusan a kowace rana ta Allah.

XS
SM
MD
LG