Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan Najeriya 500,000 Ke Gudun Hijira A Kasashen Waje - Iman


'Yan gudun hijirah
'Yan gudun hijirah

Hukumar kula da ’yan gudun hijira da wadanda yaki ya daidaita ta Najeriya ta bayyana cewa kimanin ’yan gudun hijirar Najeriya dubu 500 ne ka samun mafaka a kasashen waje.

Malama Iman Suleiman Ibrahim da ke zaman kwamishiniyar hukumar ce ta bayyana hakan a yayin wani jawabi asibitin sojoji na 44 da ke jihar Kaduna a lokacin da take rabon tallafin kekunan guragu da wasu kayayyaki ga mabukata a asibitin.

Ta ce ‘Yan gudun hijirar kasar da ke kasashe da suka hada da jamhuriyyar Nijar, Kamaru, Chadi, Mali, Libya da dai sauran kasashe masu makwabtaka da Najeriya na dakon a kwaso su a maida su gida Najeriya.

Baya ga yan gudun hijira kimanin dubu 550 da ke jiran a maido su gida, hukumar NCFRM ta yi wa sama da mutane 73,000 rijista a matsayin ’yan gudun hijira a Najeriyata wadanda suka fito daga kasashen waje 23.

Iman ta kara de cewa, kari a kan adadin mutanen da suka rasa muhallansu sama da mutum miliyan uku a cikin shekara daya, ba ya rasa nasaba da matsalar rashin tsaro da Najeriya ke ci gaba da fuskanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar NCFRM tare da hadin gwiwar kungiyar matan sojoji da ’yan Sanda ta kasar wato DEPOWA ne suka bayar da tallafin a matsayin shirin hukumar na yaki da yunwa.

Iman ta kuma ce hukumar da hadin gwiwar kungiyar DEPOWA ta samar da shirin ba da tallafin ne don taimakawa da kayan abinci da ma wadanda ba na abinci ba ga masu tsananin bukata, da suka hada da jami’an tsaron da suka ji raunuka a yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su na tsaron rayuka da dukiyoyi a filin daga.

A nata bangare, shugabar kungiyar DEPOWA, Vickie Irabor, ta ce ba da tallafin wata hanya ce ta karfafawa sojojin da suka sadaukar da rayukansu don kare al’ummar kasa da tabbatar da dorewar zaman lafiya a Najeriya.

Tun a shekarar 2009 ne jihohin Arewa maso gabas ke ta fama da matsalolin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa, duk kuwa da kokarin da gwamnatin kasar ke cewa tana yi wajen kawo karshensu, sai hare-haren 'yan bindiga dadi a yankin Arewa maso Yamma da fafutukar yan awaren IPOB a Kudu maso Gabas, da kuma masu neman kasar yarabawa a Kudu maso Yamma.

XS
SM
MD
LG