An yi ta ce-ce-ku-ce dangane da makomar Kanu wanda aka dade ba a ji duriyarsa ba tun bayan watan Yuli.
Lauyoyin da ke kare Kanu, sun yi ta kira da a fito da shugaban kungiyar ta IPOB wanda hukumomi suka gaza gabatar da shi a gaban mai shari’a Binta Nyako a zama na karshe da aka yi a ranar 26 ga wtaan Yuli.
Baya ga kin amincewa da maida Kanu Kuje, mai shari’a Binta Nyako, ta sake daga shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba mai zuwa don sauraron kararsa wanda ya kalubalanci cancantar tuhumar da ake masa.
Kanu, wanda ya ke tsare a hannun hukumar DSS tun bayan dage sauraron zaman shari’arsa a watan Yuli ya gurfana a gaban mai shari’a Binta Nyako.
A ranar Litinin hukumomin Najeriya suka yi gyara kan tuhumen da suke masa guda bakwai.
Amma a zaman na ranar Alhamis Kanu ya ki amsa aikata laifukan wadanda suka kunshicin amanar kasa da gudanar da ayyukan ta'addanci.
Jami’an tsaro dai sun hana manema labarai da wasu lauyoyi shigan cikin babbar ginin kotun da ke a unguwar central area na burnin Abuja.