Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae- in yace yana ganin alamun yiwuwar yarjejeniyar zaman lafiya da dakatar da shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa da samun taimakon kasa da kasa kan dawo da tattatalin arzikin Koriya Ta Arewa.
Firai ministan kasar Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa ya sami karfin guiwa matuka da yadda shugaba Trump ya fahimci irin lamarin nan dake sosawa al’ummar kasarsa rai
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Heather Nauert ta ce tsarin mika mulkin da aka yi a Cuba abin damuwa ne matuka ga gwamnatin shugaba Trump, saboda bana dimokradiyya bane.
Jiya Talata an samu rohotanni dake karo da juna kan ko kwararun OPCW sun issa Douma. Tawagar tana son kai ziyara gurin da ake zargin an kai harin makaman guba ranar 7 ga watan Afrilun nan wanda ya kashe akalla mutane 40.
An samu hargitsi a Majalisar Dokokin Najeriya inda wasu ‘yan daba suka shiga zauren Majalisar suka dauki sandar girma.
Jami’an Tsaro sun Yi amfani Da Barkonon Tsohuwa Wajen Tarwatsa Wani Gangamin Daliban Jami’ar Yamai A Nijer.
Yau Laraba 11 aka kaddamar da rawar dajin sojoji a Nijar wanda rundunar sojan Amurka ke jagoranta da hadin gwuiwar takwarorinsu na Afirka da ake kira Flint Lock wacce aka saba gudanarwa a kowace shekara.
Shugaba Buhari a Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Ta Sake Neman Wa'adin Na Biyu
Shugaban Amurka Donald Trump ya fayyace cewa Amurka ba kokari take ta shiga wani dogon cece-kuce da kasar China kan harkokin ciniki da kasuwancin dake tsakanin kasashen ba.
Rashin sa’ar tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lulu da Silva ta kaucewa daurin shekaru 12 a gidan kaso na nufin watakila za’a daure shi nan bada dadewa ba, akalla mako zuwa, saboda wasu ka’idoji na tuhumar da ake masa kan cin hanci da rashawa.
Karshenta dai an rantsar da Julius Maada Bio a matsayin sabon shugaban kasar Sierra Leone bayanda ya lashe wani zabe mai zafi da aka kamalla.
Wasu manyan motocin safa-safa guda ukku aka hango yau Alhamis shake da mutane da kayansu suna barin harabar ofishin jakadancin Amurka dake birnin Moscow, sun tasarwa babban filin jirgin sama a daidai lokacinda wa’adin zaman kasar da Rasha ta yanke masu yake karewa.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo's ya kai ziyara cibiyar bincike ta kimiyya da fasaha ta matasa da ke Abuja, inda ya tattauna da su kan dogaro da kai.
Kungiyoyin fararen hula a jihar Damagaram dake Nijar sun gabatar da adu'o'i don neman mafita daga dokar da aka sanyawa kasafin kudin kasar na shekarar 2018
Gwamnatin shugaba Donald Trump za ta kawo karshen wani shiri da ke bai wa ‘yan asalin Liberia da ke zaune a Amurka damar kaucewa fitar da su ta anyar tursasawa daga Amurka.
Shugaba Emmanuel Macron zai yi jawabi a bikin da ake a birnin Paris don karrama Lt. Col. Arnaud Beltrame wanda ya bada kansa garkuwa. Shugaban yace, Beltrame ya mutu jarumi.
Kungiyoyin fararen hula da wasu jam'iyun siyasa na Damagaram sun gudanar da taron manema labarai
Kasar Niger ta bi sahun sauran kasashen kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma wato UEMOA wajen anfani da banki daya asusu daya.
Shugaban ‘yan sanda na yankin Austin dake jihar Texas a nan Amurka, Brian Manley yace mutumen da ake zargi da kai hare haren bama-bamai Mark Conditt ya bar bidiyo na wani sako mai tsawon mintoci 25 da ya dauka da wayarsa ta hanu kafin ya hallaka kansa.
Domin Kari