Mataimakin shugaban kasar Cuba da ya dade yana aiki da Raul Castro na shirin zama sabon shugaban kasar yau Alhamis, mutum na farko da zai zama shugaba a kasar wanda bai da dangantaka da iyalin Castro a kusan shekaru 60.
An bayyana sunan mataimakin shugaban kasar na farko, Miguel Diaz-Canal a matsayin dan takarar shugaban kasa daya tilo jiya Laraba, a cikin tsarin na kwanaki biyu da za'a kammala yau Alhamis, da kuri'ar da 'yan majalisar kasar zasu kada, daga nan a bayyana sakamakon zaben.
Matakin da aka dauka ya sabawa wanda aka saba dauka a baya, inda baki daya majalisar kasar ke zaben shugaban kasa a kuma sanar ranar. Ana gudanar da zaben kusan cikin sirri, kamar yadda manyan shuwagabanin kasar suke bukata.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Heather Nauert ta ce tsarin mika mulkin abin damuwa ne matuka ga gwamnatin shugaba Trump, saboda bana dimokradiyya bane.
Tace, "Muna son ganin cewa al'umma za su iya tofa albarkacin bakinsu a siyasar kasar, amma da alamun cewa mutane basu da tacewa. Kusan za a ce basu da zabi a zahirance saboda ba dimokradiyya ake bi ba.
Facebook Forum