Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump: Amurka Bata Kokarin Cece-Kuce Da China


Shugaban Amurka Donald Trump ya fayyace cewa Amurka ba kokari take ta shiga wani dogon cece-kuce da kasar China kan harkokin ciniki da kasuwancin dake tsakanin kasashen ba.

Bayanda China ta tafkawa Amurka harajin da ya kai na Dala milyan Dubu 50, a matsayin maida martini ga irin wannan matakin da Amurka ta dauka kwannakin baya akan China. Trump ya fayyace cewa Amurka ba kokari take ta shiga wani dogon cece-kuce da kasar China ba.

A cikin wani sakon da ya aika zuwa ga shafinsa na Twitter ne, Trump yake cewa “Ba yaki muke da China kan harakar cinikaiya ba, wannan yakin an yi shi tunda dadewa kuma mun sha kashi a sanadin shirmen wasu mutanenmu sakarkaru da suka sarrafa tsarin kasuwanci a can baya”

Trump ya ce wannan ne ya jefa Amurka a cikin gibin Dala milyan dubu 500 da take fuskanta a kowace shekara, da kuma baiwa wasu kasashe damar satar fasahohin Amurka na kimanin Dala milyan dubu 300.

Ya ce wannan ba abinda Amurka zata kyale a ci gaba da shi bane.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG