Shirin da ake mai da mutane kasashen su tilas da ake kira DED a takaice, an kara masa shekara daya, a maimakon a dakatara da shi a ranar Asabar mai zuwa.
“A yanzu Liberia ta dai na fuskantar rikici kuma ta samu gagarumin ci gaba kan maido da zaman lafiya da gwamnatin dimokradiyya,” a cewar wata sanarwar da shugaba Trump ya rattabawa hanu da fadarsa ta White House ta fitar.
A karkashin wani shirin da aka fara a shekara 1991 mai suna T-P-S ne aka tanadarwa wasu ‘yan kasar Liberia daman zama a Amurka don gujewa rikici da yakin basasar da kasarsu ke fuskanta a lokacin.
Yanzu dai shi wannan shirin hana maida ‘yan Liberia kasarsu zai kare ne ranar 31 ga watan Maris din shekara mai zuwa ta 2019.
Facebook Forum