Yau Alhamis shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in yace cin nasarar tattaunawa da Koriya Ta Arewa zai dogara ne ba kawai kan taron da za’a yi da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un kawai ne ba, amma har da taron da aka shirya yi nan gaba tsakanin Kim da shugaban Amurka Donald Trump.
Bayanan sa ya biyo bayan na Trump, jiya Laraba wanda ya baayyana kwarin guiwar cewa Koriya Ta Aarewa zata dakatar da shirin nukilliyar ta.
Trump ya bayana cewa daraktan hukumar binciken asiri Mike Pompeo ‘’sun sami jituwa sosai da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un yayin wata ganawar sirri a Pyongyang.
Da yake ganawa da manema labarai a jihar Florida, Trump ya bayyana cewa, akwai dama mai kyau ga Koriya Ta Arewa idan ta ci nasarar dakatar da shirin nukilliyar baki daya, aka kuma tabbatar cewa ba za’a iya sake farfado da shirin ba,’’ . Trump yace muna begen lokacin da za a sami zaman lafiya da ci gaba da kuma tsaro a yankin Koriya baki daya.
Facebook Forum