Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirta ta Yamma, ECOWAS, ta amince da ta dage wasu takunkumai da ta kakabawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
Duk tawagar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 za ta samu kyautar dala miliyan bakwai ($7M), kwatankwacin (Yuro Miliyan 6.4), kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Afirka ta CAF ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ma’aikatar Lafiyar ta ce harin na Isra’ila, ya auku ne a Khan Younis, wanda ke kudancin Gaza, kuma cikin wadanda su ka mutu din har da yara tara.
Shirin Taskar VOA na wannan makon, shiri ne na musanman da Muryar Amurka ta hada a game da yaki ko tashin hankali da ake fama da shi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, da kuma mawuyacin hali da mutane ke ciki sakamakon rikicin.
A cikin watannin 12 da suka gabata, shugabannin Afirka sun ziyarci hedkwatar Tarayyar Turai a Brussels da Indiya da Rasha da Amurka da Saudiyya da Afirka ta Kudu da kuma Turkiyya.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a tsakiyar Congo da ta yi sanadin mutuwar mutane 22, cikin har wasu iyalan gida daya su 10, kamar yadda wani jami’in yankin ya bayyana a ranar Talata.
Domin Kari