Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Yana Da Ikon Ayyana Dokar Ta-Baci


Yanzu haka akalla jihohi goma sha shida su ka shigar da Trump kara a kotun tarayya da ke JIhar California, amma shugaba Trump ya ce yana da ikon ayyana dokar ta-baci domin ya gina katanga a kudancin Amurka da Mexico.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya kara jaddada matsayarsa ta cewa, yana da “cikakken ikon” da zai ayyana dokar ta-baci, domin gina katanga akan iyakar Amurka da Mexico, ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba.

Ya zuwa daren Litinin, akalla jihohi 16 suka shigar da Trump kara a kotun tarayya da ke California, inda a nan ne wasu Alkalai suka yi ta watsi da duk irin matakan da shugaba Trump ke dauka cikin watanni 25 da ya kwashe yana mulki.

Amma, shugaban na Amurka, ya fada a Fadar gwamnati ta White House cewa, “yana da yakinin zai yi nasara a karar da aka shigar da shi.”

A lokacin da ya ayyana dokar ta-bacin a ranar Juma’ar da ta gabata, Trump ya ce, yana sa ran ba zai yi nasara a shari’ar farko ba, amma ya ce yana da yakinin idan batun ya je gaban kotun kolin kasar, kotun za ta yi watsi da duk wani hukunci da wata karamar kotu ta yanke.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG