Ministar tsaron kasar Venezuela, ya ce dakarun kasar za su ci gaba da zama akan iyakokin kasar, kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce, “za su iya amfani da kowanne irin zabi” domin ganin an samar da gwamnatin wucin gadi a kasar ta Venezuela.
A jiya Talata, ministan tsaron kasar, Vladimir Padrino, ya yi watsi da kalaman Trump a wani jawabi da ya yi ta talbijin, yana mai cewa, furucin shugaban “babu dattaku a cikinsa, sannan ba a taba yin irinsa ba.”
“Waye shugaban dakarun kasa da doka ta yarda da shi? Suna tunanin sune ke da kasar nan, kuma Donald Trump ya yi tunanin yana da karfin ikon da idan ya ba da umurni, dakarunmu za su bi?” inji shugaba Nicolas Maduro.
A ranar Litinin, yayin da yake jawabi a gaban ‘yan kasar Venezuela mazauna nan Amurka a jihar Florida, shugaba Trump, ya yi kira ga dakarun Venezuela, da su yi watsi da umurnin shugaba Maduro, su amince da tayin afuwa da shugaban wucin gadi Juan Guaido ya yi musu.
Facebook Forum