Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria: Farmakin Baghuz Ya Fuskanci Tsaiko


Wani sojan gamayyar dakarun SDF da Amurka ke marawa baya a kauyen Baghuz. Ranar 18 Fabrairu 2018.
Wani sojan gamayyar dakarun SDF da Amurka ke marawa baya a kauyen Baghuz. Ranar 18 Fabrairu 2018.

Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka, sun bayyana cewa samun karin fararen hula a yankin, wadanda mayakan ke amfani da su a matsayin garkuwa, shi ne dalilin da ya sa farmakin ke tafiyar hawainiya.

Farmakin da ake kai wa a tunga ta karshe da ke hannun mayakan IS wanda suka ayyana a matsayin daularsu a Siriya, ya fuskanci tsaiko, yayin da aka shiga yini na uku.

Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka, sun bayyana cewa samun karin fararen hula a yankin, wadanda mayakan ke amfani da su a matsayin garkuwa, shi ne dalilin da ya sa farmakin ke tafiyar hawainiya, kamar yadda mai magana da yawun gamayyar dakarun ta SDF, Mustapha Bali, ya wallafa a shafin Twitter.

Sai dai bai bayyana matakan da suke dauka ba, domin ganin an an fitar da fararen hular daga Baghuz ta hanyar da ba za su cutu ba.

Amma dai ya yi gargadin cewa, jinkirin da aka samu ba zai dauki dogon lokaci ba.

Akalla sojoji dubu 15 da ke samun goyon bayan Amurka a Siriya sun kaddamar da wani mummunan hari a wani guri dan karami da ke kauyen Baghuz na arewa maso gabashin Siriya a ranar Juma’a da daddare, wanda ya samu goyan bayan jiragen yakin Amurka da na kawayenta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG