Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Damke Wadanda Ake Zargi Da Kai Hari A Yankin Kashmir


Jami'an kasar Pakistan a taron manema labarai
Jami'an kasar Pakistan a taron manema labarai

Bayan wani hari da aka kai a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India, wanda ya hallaka mutane da dama, yanzu haka Pakistan ta ba da sanarwar damke shugaban kungiyar da ake zargi da kai harin.

Hukumomi a Pakistan sun damke wasu mutane 44 da ake zargin ‘yan bindiga ne, cikinsu har da wani dan’uwan jagoran wata kungiya mai tsattsauran ra’ayi, wadda kasar ta Indiya ke zargi da kai harin kunar bakin wake da wata mota a yankin Kashmir mai rabuwar kawuna.

Mummunan harin da aka kai gundumar Pulwama ranar 14 ga watan jiya na Fabrairu, ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaron Indiya wajen 40, al’marin da ya yi kusa haddasa yaki tsakanin kasashen biyu masu makaman nukiliya, saboda zargin cewa kungiyar Jaish-e-Mohammed da ke kasar Pakistan ce ta kai harin.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Pakistan Shehryar Afridi ya gaya ma manema labarai jiya Talata cewa wadanda aka damke din sun hada da Mufti Abdul Rauf, dan’uwan Massood Azhar, shugaban kungiyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG