Yanzu haka hukumomin Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bakin Haure, sun shirya wani taron fadakar da matasa a birnin Tawa (Tahoua), inda aka baje kolin ire iren ayukan da za su iya yi a cikin kasar, da ya hada da ayyukan hannu da noman rani ko na damina, domin a fitar da tunanin zuwa kasashen Turai, abinda ya ke janyo rasa rayuka a cikin sahara da kuma Teku.
Daraktan fadar ministan da ke kula da samarwa matasa kasar ayyuka y ace, wannan taron zai bada damar bunkasa ayyuka ga masu burun bude masana’antu tare da kuma zaburar da matasa suma su bude nasu ayyukan yi.
Haka kuma ya ce sun fadakar da su game da ayyukan da ake iya yi cikin kasar, sannan ya kara da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga gwamnati.
Gwamnan jihar Tahoua, Malam Musa Abdurahamane, ya ce wannan taron ya na da matukar muhimmanci ga matasan kasar, saboda samun damar koyon ayyukan yi domin dogaro da kai a cikin kasar, ba sai sun tafi kasashen Turai ba.
Wasu daga cikin matasan suma sun bayyana jin dadin wannan tsari da aka bullo dashi na koyon ayyukan yi, sun kara da cewa lallai matasa ba za su fita su tafi kasashen waje ba neman wani abu, inda su ka yi kira da gwamanati ta kara ba su tallafi da kuma goyon baya.
Har ila yau hukumomin jamhuriyar Nijar sun ja damarar ganin sai yadda hali yayi, amma za su ci gaba da tallafawa abokan huldar su na Turai wajen dakatar da bakin haure zuwa arewacin kasar.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Facebook Forum