Ganin yadda 'yan-bindiga ke cigaba da afkawa garuruwa da kuma sace mutane don neman kudin fansa duk da matakan da gwamnonin Arewa maso yamman su ka dauka ya sa wasu kiran sauya salo.
A Najeriya bayanai na nuna cewa bijerewa ga umurnin jagoranci da wasu fulani suka yi fiye da shekaru dari biyu da suka gabata shine ya haifar da zaman su cikin jeji har suka nisanta da jama'a.
Mai martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya jaddada cewa duk wadanda ke daukan makami suna kisan jama’a da sunan addini, zasu fuskanci mummunan hukunci daga Allah.
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) na shirin gudanar da wani babban taron gaggawa na musamman kan kasar Guinea da za a fara ranar 9 ga watan Satumba a Accra babban birnin kasar Ghana.
Yau 1 ga watan satumba al’umar jihar Tilabery ta fara amfani da babura bayan dage dokar haramcin da hukumomin jamhuriyar Nijer suka kafa a shekarar 2018 a matsayin wani bangare na dokar ta bacin da aka kafa da nufin warware matsalar tsaron da ake fama da ita.
Yau Laraba, wani alkalin babbar kotu a Dar Es Salaam ya ce za’a iya ci gaba da shari’ar ta’addanci kan shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Tanzania kamar yadda aka tsara, inda ya yi watsi da korafe-korafe daga jam’iyarsa.
Hukukamar yaki da fataucin bil’adama da bautar da mutane ta Najeriya, NAPTIP ta kaddamar da kwamitin ka-ta- kwana da aka dorawa alhakin murkushe ayyukan masu sata da safarar mutane zuwa kashen katere a yankin arewa maso yammacin kasar.
Turkiyya ta yi alƙawarin ƙarfafa dangantakarta da Najeriya domin taimaka mata wajen magance matsalar ta'addanci da yaki ci yaki cinyewa a kasar musamman ma aika aikar 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabas.
Masana kimiyya a Afirka ta Kudu sun ce sun gano sabon nau'in COVID-19.
Wasu 'yan asalin yankin kudu maso gabashin Najeriya na cewa tsoro ne ya sa akasarin al'ummar yankin ke ci gaba da zaman gida a kowace ranar Litinin, duk da cewar kungiyar IPOB mai fafutukar tabbatar da kasar Biafra da ta ba da umurnin, ta riga ta dakatar da wannan shirin.
A jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fafitikar kare muhalli sun gudanar da wani taron hadin gwiwa da jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin kasa da kasa.
Jakadan Najeriya a Rasha, Farfesa Abdullahi Shehu ya bayyana cewa Najeriya da Moscow sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi sayen kayan aikin soja.
“Rahoton ya kunshi duk binciken da aka yi kan lamarin, hujjoji, da kuma bahasin da DCP Abba Kyari ya bayar da na sauran mutanen da lamarin ya shafa.” Sanarwar ta ce.
An nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a matsayin shugaban Jami’ar Cavendish ta kasar Uganda a hukumance.
Wasu yan Majalisar Dokokin kasa da Kwararru a fanin zamantakewan dan Adam sun mayar da martani akan makomar dubban yan Kungiyar Boko Haram da ke ta mika wuya, inda suka bada shawarwari akan matakan da za a dauka a kansu kafin a mika su ga al'umma.
Kamaru ta mayar da gine -ginen jama'a da ke kan iyakarta da arewacin Najeriya zuwa matsugunan tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba. Daruruwan 'yan Boko Haram na ficewa daga kungiyar da suka hada da sama da dari biyu ranar Lahadi.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijer sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda a kalla 100 a yayin wata rawar dajin da suka yi a kewayen kauyen Boni dake iyakar Nijer da Burkina Faso lamarin da ke kara karfin gwiwa ga al’uma a wannan lokaci da ‘yan bindiga suka hurawa fararen hula wuta.
Wani rahoton da kungiyar Amnesty international ta fitar a jiya talata na nuni da cewa makaman da reshen kungiyar IS da na Alqaida ke amfani da su a yakin da ake gobzawa a yankin sahel har ma da wadanda ‘yan aikin sa kai ke rike da su kirar Nahiyar Turai ne.
Shida daga cikin dalibai 136 da aka yi garkuwa da su daga wata makarantar Islamiyya da ke jihar Neja a arewa maso tsakiyar Najeriya sun mutu sakamakon rashin lafiya, kamar yadda shugaban makarantar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin.
Domin Kari