Shugaban jam’iyyar Chadema, Freeman Mbowe, da magoya bayan sa sun bayyana tuhumar a matsayin bita da kullin siyasa ne don murkushe masu adawa, kana sun zargi ‘yan sandan da azabtar da shi a tsare.
Lauyoyinsa sun bayar da hujjar cewa sashin cin hanci da rashawa na babbar kotun inda ya bayyana ba shi da ikon sauraron karar, wanda a baya kotun majistare ce ke kula da shi.
Amma kuma yau Laraba, mai shari’a, Elinaza Luvanda ya ce, “wannan kotun tana da hurumin sauraron karar ta’addanci saboda haka ban yarda da rashin amincewa daga masu kare shi ba.”
Shari’ar an gudanar da ita cikin tsauraran matakan tsaro, tare da wasu wakilai daga ofisoshin jakadancin kasashen waje da manyan shugabannin jam’iyyar Chadema suka halarta, amma ‘yan sanda sun hana ‘yan jarida da dama shiga zauran kotun.