Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Menene Makomar Tubabbun Yan Boko Haram?


Wasu mayakan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu mayakan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Wasu yan Majalisar Dokokin kasa da Kwararru a fanin zamantakewan dan Adam sun mayar da martani akan makomar dubban yan Kungiyar Boko Haram da ke ta mika wuya, inda suka bada shawarwari akan matakan da za a dauka a kansu kafin a mika su ga al'umma.

An kwashi sama da shekaru 11 ana fama da ta'addancin yan Kungiyar Boko Haram a Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, inda a yanzu kididdiga ta nuna cewa, ana da yan gudun hijira sama da miliyan 2 da ke zaune a sansanoni, sakamakon munanan ayyukan da yan ta'addan suka aikata, baya ga dubban wadanda suka rasa rayukan su.

Wani abu da ya dauki hankali yanzu shi ne bayanan da ake ta samu daga Arewa Maso Gabashin Najeriya da ke nuni da cewa, yan kungiyar Boko Haram 2.600 ne suka mika wuya ga sojojin kasar, wanda mahukunta ke ta tuntu6ar juna akan matakin da za a dauka, wa'ya Allah tsugunad da su za a yi, ko a bari wadanda suka tuba su koma ga iyalan su kai tsaye?

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan ya yi tsokaci cewa shi bai yarda a amayar da su cikin al'umma kai tsaye ba. Lawan ya ce a natsu a tantance wadanda suka tuba, sannan a tsugunad da su a wani wuri na daban har zuwa wani lokaci , sannan in an ga yadda rayuwar su ta kasance, sai a iya mayar da su cikin al'umma.

Shi ma Senata Mai wakiltan Jihar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa kuma shugaban komitin kula da harkokin soji, Sanata Ali Ndume yana mai ganin akwai mataki da mahukuntan kasa za su dauka da kowa ba zai cutu ba, duba da yadda yanzu haka ake rikon tubabbun a wasu wurare na daban.

Ndume ya ce Gwamnan jihar Borno yana ganawa da Shugaban kasa akan matakan da za a dauka, kuma nan ba da jimawa ba za a fito da tsari da kowa zai gamsu da shi saboda akwai wadanda aka sa su a cikin ta'addancin ba tareda son ran su ba. Ndume ya ce irin wadannan ya kamata a yi masu adalci.

Amma mai fashin baki a al'amuran zamantakewan dan Adam Mohammed Ishaq Usman ya ce ko mi za a yi, kar a yi sulhu da yan ta'adda domin babu inda aka ce a yi sulhu da wanda ba ya mutunta rai. Usman ya ce maciya amana ne yan ta'adda saboda haka bai kamata a yi sulhu da su ba.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a daidai lokacin da gwamnati za ta dauki mataki akan makomar tubabbun yan ta'addan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG