Shugaba Vladimir Putin ya gargadi Amurka da kawayenta akan cewar Moscow na duba yiyuwar maida martani da makaman nukiliya matukar suka bari Ukraine ta kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka kera a kasashen yammacin duniya
Guguwa Helene da ta ratsa jihohin Florida da Georgia cikin daren Juma’a na da ya daga cikin irinta mafi karfi da aka gani a tarihin Amurka, inda ta hallaka mutum guda tare da haddasa ambaliyar ruwa a unguwanni da katse wutar lantarki ga fiye da gidaje da kantuna miliyan biyu
A yau Alhamis, Isra’ila ta yi fatali da shawarar tsagaita wuta tsakaninta da Hezbollah, inda ta bijirewa kawayenta ciki har da Amurka da suka bukaci a dakatar da yaki nan take na tsawon makonni uku domin bada damar yin amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen kaucewa fadadar yakin
A yau Laraba, tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewar rayuwarsa na fuskantar barazana daga kasar Iran bayan da tawagar yakin neman zaben jam’iyyar Republican ta ce jami’an leken asirin Amurka sun gargade shi game da barazana ta zahiri da ta takaita a kansa daga birnin Tehran
A yau Laraba Majalisar Dattawan Najeriya ta tabattar da ai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya
Da safiyar yau Laraba, kungiyar Hezbollahi ta cilla dimbin makaman roka zuwa cikin Isra’ila, ciki harda wanda ta harba kan birnin Tel Aviv wanda ya kasance hari mafi nisa dake alamanta sake kazancewar yaki biyo bayan kisan daruruwan mutane da hare-haren Isra’ila kan Lebanon suka yi.
Isra’ila da kungiyar Hizbullahi sun cigaba da musayar wuta a yau Talata yayin da adadin mutanen da munanan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa suka hallaka ya haura kusa da 560 sannan dubban mutane sun arce daga yankin kudancin Lebanon inda bangarorin biyu ke daf da fadawa cikin kazamin yaki
A yau Talata shugabannin kasashen duniya zasu kaddamar da taron da suke yi a duk shekara a babban zauren MDD a karkashin maudu’an da suka hada da karuwar rabuwar hannu tsakanin al’ummar duniya da manyan yake-yaken dake gudana a Gaza da Ukraine, Sudan da kuma barazar yakin yankin Gabas ta Tsakiya
Ana cigaba da neman mutanen da ake zargi da hannu a harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4 tare da jikkata wasu 17 a jihar Alabama.
A yau Litinin Isra’ila ta kaiwa wuraren Hizbullahi fiye da 100 hari ta sama, al’amarin da hukumomin lafiyar Lebanon suka ce ya hallaka akalla mutane 182, inda ta kasance rana mafi muni a kasar a rikicin da kungiyar dake samun goyon bayan kasar Iran ta shafe kusan shekara guda tana yi.
Domin Kari