Bayan wasu daga cikin mafi munin musayar wuta akan iyakokin kasashen 2, Isra’ila ta gargadi jama’a su kauracewa wuraren da tace kungiyar mai gwagwarmaya da makamai ke boye makaman nata.
Bayan kusan shekara guda da kaddamar da yaki akan kungiyar Hamas ta zirrin Gaza dake iyakarta ta kudu, Isra’ila ta fara juya akalarta zuwa iyakarta ta arewa, daga inda kungiyar Hizbullahi ke kai harba mata makaman roka domin taimakawa kawarta hamas.
“Wannan mataki zai cigaba har sai mun cimma burinmu na mayar da mazauna yankin arewacin kasarmu gida cikin lumana,” a cewar Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant a bidiyon da ofishinsa ya wallafa, abinda ya shata fagen rikici mai dogon zango kasancewar hizbullahi ta sha alwashin cigaba da yaki har sai an tsagaita wuta a zirrin Gaza.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna