Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Na Neman Wanda Ake Zargi Da Harbin Bindigar Da Ya Kashe Mutane 4 A Alabama


Birmingham, Alabama, Sept. 22, 2024.
Birmingham, Alabama, Sept. 22, 2024.

Hukumomi basu ba da rahoton kama kowa ba bayan harbin kan mai uwa da wabin da ya hallaka mutane 4 tare da jikkata wasu 17, al’amarin da ‘yan sanda suka bayyana da shiryayyen harin da maharba da dama suka bude wuta don neman ran mutum guda a wajen wani shahararren wurin holewar dare dake Alabama.

Alabama
Alabama

Harbin daya faru da maraicin Asabar din data gabata a shahararren wurin shakatawar “Five Points” dake kudancin gundumar Birmingham ya tarwatsa yankin mai yawan wuraren cin abinci da shaye-shaye da aka sani da hada-hada a dararen karshen mako.

Harin bindigar ya gefen titin dake wajen Hush, wani gidan saukar baki dake gundumar shakatawar, inda har izuwa safiyar jiya lahadi ana ganin jini a gefen titin dake wajen wurin.

Birmingham, Alabama, Minggu, 22 September 2024. (Bill Castle/WBMA via AP)
Birmingham, Alabama, Minggu, 22 September 2024. (Bill Castle/WBMA via AP)

Baturen ‘yan sanda Scott Thurmond yace hukumomi sun yi amanar cewa an kai harin ne don neman hallaka daya daga cikin mutanen da suka mutu, mai yiyuwa ‘yan ina da kisa ne suka kai shi. Mota ce ta tsaya sai mahara da dama suka fito suka bude wuta, sannan suka arce, a cewarsa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG