Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta cafke makamin rokar, abinda ya sabbaba tashin jiniyar ankarar da kawo hari a birnin Tel Aviv da fadin Isra’ila. Ba’a samu rahoto kan irin barnar da harin yayi ba.
Rundunar sojin ta ce ta maida martani ta hanyar kai hari yankin kudancin Lebanon wurin da aka harbo makamin rokar.
Hezbollhi ta ce ta harba makamin rokar ne tana harin shelkwatar hukumar leken asirin Isra’ila, Mossad, wacce take zargi ta kitsa jerin kashe-kashe akan manyan kwamandojinta a baya-bayan nan da kuma harin fashewar na’urorin sadarwa na makon da ya gabata wanda ya hallaka gommai tare da jikkata dubban mutane, ciki har da mambobin kungiyar da dama.
Rundunar sojin Isra’ila tace wannan shine karon farko da makamin da aka harbo daga Lebanon ya isa tsakiyar kasar.
Kungiyar Hezbollahi dai ta yi ikrarin kai hari kan wata cibiyar tattara bayanan sirri dake kusa da Tel Aviv a wani hari da ta kai ta sama a watan da ya gabata, saidai ba’a tabbatar da harin ba.
Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta sha kai hari kan birnin Tel Aviv a watanni farko bayan fara yakin.
Harin ya kara zafafa zaman dar-dar din da ake ciki, inda ta bayyana cewar yankin na daf da afkawa cikin yaki, kuma Isra’ila ta ci gaba da kaiwa kungiyar Hamas dake birnin Gaza hari.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna