Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Mutanen Da Hare-Haren Isra’ila Ta Sama Suka Hallaka A Lebanon Sun Kai 560


Lebanon
Lebanon

Isra’ila da kungiyar Hizbullahi sun cigaba da musayar wuta a yau Talata yayin da adadin mutanen da munanan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa suka hallaka ya haura kusa da 560 sannan dubban mutane sun arce daga yankin kudancin Lebanon inda bangarorin biyu ke daf da fadawa cikin kazamin yaki

Iyalan da suka rasa muhallansu na kwana a matsugunai marasa inganci da aka kafa a Beirut da birnin Sidon dake gabar teku. Inda aka kakkame dakunan otel-otel ko kuma farashinsu yafi karfin iyalai da dama, wadanda basu da matsuguni su rika kwana a motocinsu, a dandali koma a gabar teku.

ISRAEL-LEBANON
ISRAEL-LEBANON

Issa Baydoun ya tsere daga kauyen Shihine dake kudancin Lebanon sa’ilin da hare-haren bama-bamai suka afka masa. Ya iso Beirut cikin jerin gwanon motocin tare da danginsa. inda suka rika kwana a cikin motoci a gefen tituna bayan da suka fahimci cewar dukkanin wuraren kwana sun cika makil.

“Mun sha bakar wahala a hanya kafin mu iso nan,” a cewarsa.

“Mun bar gidajenmu kasancewar Isra’ila na auna fararen hula tare da kai musu hari,” a cewarsa, wannan shi yasa muka baro gidajenmu, domin baiwa ‘ya’yanmu kariya.”

Masu yi mana fatan alheri sun yi mana tayin gidaje ko dakunan da babu kowa a ciki a shafukan sada zumunta, yayin da masu neman lada suka kafa wuraren girke-girke a wani gidan mai da aka daina amfani da shi a wajen birnin Beirut domin dafawa ‘yan gudun hijira abinci.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG