Kamar sauran jihohin Najeriya duban masu zabe ne suka fito domin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a birnin legas. Sai dai kuma jama'a da suka fito wannan zabe basu kai na zaben shugaban kasa ba da aka gudanar makwanni uku da suka gabata ba.
Sai dai duk da umurnin da babban bankin ya bayar, rahotanni sun ce har yanzu akwai wasu ‘yan Najeriyar da ke dari-darin karbar kudaden.
Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga Abeokuta yana kan hanyarsa ta shiga Legas a lokacin da hatsarin ya auku.
Bayan ayyana ‘dan takaran jamiyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudar a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu, an fara wasu shagulgulan murna.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar legas ta bayyana sunan dan sandan da ya harbe wata lauya mai juna biyu a ranar Kirsimati kuma tuni ya shiga hannun hukuma.
Domin Kari