Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wasu Mazauna Legas Suke Shagulgulan Murnar Nasarar Da Tinubu Ya Samu

Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas

Bayan ayyana ‘dan takaran  jamiyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudar a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu, an fara wasu shagulgulan murna.

LEGAS, NAJERIYA - Magoya bayan Jami'yyar ta APC da ‘dan takarar sun bazama akan titunan birnin Legas da sauran Jihohin kasa, domin gudanar da shagulgulan murnar domin godiya da wannan nasara da suka samu na lashe zaben shugaban kasa.

Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas

To yanzu dai za'a ce bakin cikin faduwar APC a Jihar Legas a wancan zabe yanzu ya kona farin ciki, tunda ‘dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu daga karshe ya lashe zaben tare da zama shugaba mai jiran gado kamar yarda shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya ayyana shi.

Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas

To ko yaya mazauna birnin Legas ke ji da wannan nasara? Akasain wadanda Muryar Amurka ta zanta dasu dai sun bayyana jin dadin su tare da kiran hadin kai tsakanin ‘yan adawa domin ciyar da kasar gaba, a wannan lokaci da ake neman zaman lafiya da ci gaba a kasar.

Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas
Anfara Gudanar Da Shagulgulan Murnar Sabon Shugaban Kasa A Jihar Legas

Yanzu dai abun jira a gani shine ko Jamiyar zata samu nasara a zaben gwamnoni mai zuwa.

Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibrin:

Yadda Wasu Mazauna Legas Suke Shagulgulan Murnar Nasarar Da Tinubu Ya Samu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG