LAGOS, NIGERIA - Dan sanda mai mukamn ASP ya harbe lauyar ce mai suna Barista Bolanle Raheem.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta sanarwar da kama ASP Drambi Vandi na rundunan ‘yan sanda ta Ajiwe dake unguwan Ajah a Legas bisa tuhumar sa da kisan kai.
A wata sanarwa da kakakin rundunan, Benjamin Hundeyin ya fitar, rundunar ta ce tuni kwamishinan ‘yan sanda jihar ya bada umarnin a aika da shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar dake Yaba domin yi masa tambayoyi.
Bincike ya nuna cewa wannan bashi ne karon farko ba da ake samun kisan kai daga wannan ofishin ‘yan sandan na Ajah ba, domin ko a farkon watan Disamba wani dan sanda da har yanzu aka ce ba a san kowa nene ba, ya harbe wani mutun mai suna Gafaru Buraimoh har lahira inda ake ci gaba da bincike.
Musa Jika, mai fafutukar kare hakkin bil’adama a Najeriya, ya ce sun samu labarin wannan lamari da ya faru kuma suna suka akan aika-aikan da ake zargin dan sanda da aikatawa, kuma ya kamata a duba wani hali ma yake ciki ya dauki wannan mataki.
Musa Jika ya ce za su dauki matakan bin kadin lamarin da ya faru kuma suna bukatar gudanar da bincike daga rundunan ‘yan sandan Najeriya da ma gwamnati.
Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibril: