Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Fito Zaben Gwamna A Jihar Legas Kamar Na Shugaban Kasa Ba


Zaben 2023
Zaben 2023

Kamar sauran jihohin Najeriya duban masu zabe ne suka fito domin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a birnin legas. Sai dai kuma jama'a da suka fito wannan zabe basu kai na zaben shugaban kasa ba da aka gudanar makwanni uku da suka gabata ba.

LEGOS, NIGERIA - Tunda sanyin safiya ne dai masu zabe suka fara isa cibiyoyin zabe duk da cewa dai malaman zabe sun makara don haka ba ko ina ne aka fara zabe da wuri ba.

Gwamnan legas Babajide Sanwo Olu ya kada kuri'ar sa ne a mazabar titin Lateef Jakonde dake Ikoyi a Legas tare da mai dakin sa. Suma ‘yan takaran Labour Party da PDP sunyi zaben ne a mazabun su.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu (Facebook/Gwamna Sanwo-Olu)

Dukkannin su sun yaba da yadda ake zaben cikin nasara.

Wasu masu zabe da muka tattauna dasu, irin su Malam Nura Sufiyanu ya ce zabe an yi shi cikin lafiya, sai dai mutane basu fito ba, kuma dama basa fitowa.

Itama wata mata Hajiya Halimatu Usman, kira tayi da a fito ayi zabe kuma a barwa Allah komai domin samun shugabanni na kwarai.

Ta bangaren jami'an tsaro kuma an saka su lunguna da sakuna na birnin, banda wayanda ke shawagi ta jiragen sama.

Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibril:

Mutane Ba Su Fito Zaben Gwamnoni A Jihar Legas Kamar Na Shugaban Kasa Ba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG