A Uganda kotu ICC ta samu tsohon kwamandan ‘yan tawayen Lord Resistance Army, Dominic Ongwen da aikata laifuka 61 da suka hada da laifin yaki da kisan mutane. Ya na fuskantar yiwuwar daurrin rai-da-rai.
A DR Congo, ‘yan majalisar dokoki sun zabi sabon kakakin majalisar wanda ke biyayya ga shugaba Felix Tshisekedi, biyo bayan yunkurin karya karfin iko da tsohon shugaba Joseph Kabila ke da shi a majalisar.Mai gabatarwa Abdoulaziz Adili Toro
A Burkina Faso wasu yara sun zama na farko a tarihin kasar da aka yi wa tiyata a zuciya. Wannan wani abu ne mai muhimaci a cewar likitocin kasar kuma zai iya sauya kallon da akewa likitoci a yammacin Afrika
A Amurka shugaba Joe Biden ya kai ziyarar jaje a majalisar dokokin kasar domin karama Brian Sicknick, dan sandan majalisar da ya mutu lokacin da magoya bayan tsohon shugaba Donald Trump suka danna majalisar.
Mazaunan birnin Maiduguri a Najeriya su na ci gaba da fama da rashin lantarki bayan mayaka masu da’awar jihadi sun lalata na’urorin samar da wuta, abinda ya kawo karancin ruwa da kawo cikas ga rayuwar yau da kullum. Mai gabatarwa Abdoulaziz Adili Toro.
A Vietnam shugaba Nguyen Phu Trong, mai shekaru 76 ya kare manufar jam’iyyarshi na yaki da cin hanci da rashawa, bayan da aka sake zaban shi a wani wa’adi na uku.
Kungiyoyin rajin kare dimokradiya sun kaddamar da ayyukan fadakar da jama’a tare da tunatar da masu hannu akan sha’anin gudanar da zabe
Akalla mutane tara da suka hada da wani janar na soja sun mutu, wasu 15 kuma suka jikkata a wani harin da kungiyar Alshabab ta kai a wani otal a Moghadishu.
Sojojin Myammar sun kwace ikon kasar a yau Litinin karkashin dokar ta-baci da aka sanya na shekara guda, saboda rashin daukar mataki kan korafin da suka yi cewa an yi magudi a zaben da aka gudanar a watan Nuwamba.
Shugaban Amurka Joe Biden na shirin karbar bakuncin wasu sanatoci 10 ‘yan jam’iyyar Republican don tattaunawa yau Litinin game da wani sabon zagaye tallafin tattalin arzikin coronavirus.
A Najeriya sabon babban hafsan tsaron kasar Manjo Janar Leo Irabor, ya kai ziyara babbar cibiyar yaki da Boko Haram dake Maiduguri, bayan shugaban kasar ya sauya manyan hafsoshin sojin kasar.
Makiyaya da masana dokokin kasa sun mayar da martani ga kiran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na samar da dokar da zata haramtawa Fulani makiyaya shiga yankin kudancin da sunan kiwo.
Sai kuma Najeriya inda Saudiya ta taso keyar daruruwan ‘yan Najeriya da suka je kasar domin yin aiki, bayanda VISA din su ta kare. Wasun su sun ce an kuntata musu yayin da suke jiran komawa gida
A Birtaniya daga ranar juma'ar nan, kasar ta haramta sauka da tashin jiragen fasinja zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, abin da ya sa kasar ta rufe hanyar zirga-zirga mafi hada-hada a duniya. Hakan ya na zaman wani mataki na dakile sabon nau’in Covid-19 daga Afrika ta kudu.
Shugaba John Magfuli na Tanzania ya kalubalanci sahihancin wasu magungunan rigakafin Covid19, ya na mai cewa wasu alluran ba su da alheri ga kasarshi, kuma masu neman alluran a kasashen waje, su ke dawowa da cutar kasar.
Kasar Iran ta samar da sinadarin uranium da ta sarrafa kilogram 17 daga kashi 20 bisa dari cikin kasa da wata daya, abinda ya sa kasar ke kusa da matakin yin makamin nukiya yayin da zaman dar-dar da Amurka ke karuwa.
Papa Roma Francis ya yi yawabi a fadar Vatica na cika shekaru 76 da ‘yantar da mutane a sansanin mutuwa na Auschwitz inda ‘yan Nazi suka kashe yahudawa fiye da miliyan daya.
Domin Kari