A Amurka masu shigar da kara na jam'iyyar Demokrat sun yi wani tataki a ginin majalisar dokoki na Capitol domin gabatar da tuhumar tsige tsohon shugaba Donald Trump a majalisar dattijai.
AUganda jagoran ‘yan adawa Bobi Wine yayi Allah wadai da ‘ukuba” da “cin mutunci” da ya ce an yi mushi bayan jami’an tsaro sun janye kawanyar da suka yiwa gidanshi tun bayan zaben shugaban kasar.
‘Yan fashin kan teku a Najeriya sun kama matukan jirgin ruwa ‘yan Turkiya su 15 sannan suka kashe wani dan Azerbaijan daya. Ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce har yanzu ‘yan fashin bas u tuntubi hukumomin kasar ba.
Dan Najeriya mazaunin kasar Amurka Dr Safiyanu Saidu Ali ya yi hira da Sashen Hausa na muryar Amurka kan ranstarda shugaba Joe Biden da kuma Kamala Harris.
Hira ta musamman da 'yan Afrika mazaunan kasar Amurka akan wannan ranar
A Burtaniya dai: Maganin an dakatar da ci gaba da gwajin maganin Astrazeneca na COVID-19 na wucin gadi, bayan daya daga cikin wadanda ake yin gwajin maganin a kansu ya kamu da wani ciwo da ba a gano shi ba.
Yankin Somaliland wanda ya balle, ya bude ofishi a Taipei yau a Taiwan, a wani mataki da ba'a saba gani ba biyo bayan tsamin danganatakar dipilomasiyya da Beijing.
A Senegal ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi karshen mako a birnin Dakar, ya yi sanadiya mutuwar mutum 4, hakan dai ya sa wasu na sukar gwamnati da rashin daukan mataki.
A Spain a yau litinin kasar ce ta farko a kasashen turai da aka samu mutum 500,000 da suka kamu da Korona. Ma'aikatar lafiya ta ce an samu karin wadanda aka kwantar a sibiti masu dauke da cutar.
A India: Asibitocin New Delhi na fuskantar kalubale bayan watanni shida ana samun karuwar cutar COVID-19, yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya haura miliyan 4.2, inda ta shiga gaban Brazil a matsayin ta biyu da ta fi yawan masu cutar a duniya.
A Rwanda: Shugaba Paul Kagame ya ce Paul Rusesabagina, wanda ya fito a matsayin gwarzo a fim din "Hotel Rwanda" kuma mai sukar gwamnati, zai gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da goyon bayan tashin hankali na 'yan tawaye.
Najeriya na shirin samar da kamfanonin hakar albarkatun kasa 50 nan da shekarar 2023, da zummar maye gurbin asarar da COVID-19 ta janyo. A cewar ministan albarkatun kasar Olamilekan Adegbite.
A Iraqi shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya gana da takwaransa Barham Salih, ya kuma ayyana cewa babban kalubale da kasar ke fuskanta shi ne ‘yan ta’adda, da kuma shishigin kasashen ketare.
A Guine kuwa: Jma’iyyar da ke mulki ta tabbatar da jita-jitar da ke yawo, cewar shugaban kasar Alpha Conde mai shekaru 82 da haihuwa zai nemi tazarce karo na uku, wanda hakan ya haifar zanga-zanga.
A Afghaninstan: Wani bom ya tashi a wata mota kusa da ofishin ‘yansanda da ke Gardez a yau, ‘yan sanda 3 sun mutu wasu 5 sun raunata. “yan kungiyar Taliban sun dauki alhakin harin.
A Sudan ta Kudu, gwamnatin kasar ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyar na kasar a ranar Litinin. An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Juba da ke Sudan ta Kudu.
A Italiya, akalla bakin haure uku ne suka rasa rayukansu yayin da aka nemi guda daya da aka rasa bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kama da wuta a tekun Ionian, kusa da gabar tekun Italia ranar Lahadi.
Domin Kari