Daruruwan ‘yan bindiga sun yi dirar mikiya a garin Amarawa na yankin Illela ta gabashin Sakkwato inda suka hallaka mutane da dama kuma suka sace wani mutum.
Jam’iyyun kawancen hamayya a jamhuriyar Nijer sun lashi takobin ganin an bai wa dan takararsu Mahaman Ousman nasarar da su ke ikirarin ya samu a fafatawar da ta hada shi da Bazoum Mohamed a ranar 21 ga watan Fabrairu sai dai jam’iyyar PNDS mai mulki na cewa a hadu a kotu domin ta raba gardama.
A Ethiopia wata wuta da aka kuna da gangan ta lalata gine gine fiye da dari biyar a wannan mako kusa da garin Gijet, kamar yadda wani bincike na Reuters da kuma hotuna suka nuna, abin da ke gasganta rahotannin cewa ana ci gaba da rikici a wasu yankunan Tigray.
A jamhuriyar Nijar aka sanar da dan takarar jam'iyya mai mulki Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa yayinda magoya bayan yan adawa suka ce an tafka magudi inda suka ci gaba da kona tayoyin mota akan tittuna.
Amurka na gab da samun mace-mace rabin miliyan sakamakon cutar COVID-19, da karin mace-mace da ke da alaka da coronavirus fiye da kowacce kasa, a cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins.
A Jamhuriyar Nijar jami'an hukumar zaben ke ci gaba da kilga kuri'u zagaye na biyu na zaben shugaban kasar tsakanin Mohamed Bazoum da kuma Mahaman Ousman. Wannan kuma na zuwa ne bayan mutuwar mambobi 7 na hukumar inda motarsu ta taka wani bam dake kan hanya.
Dakarun hadin gwiwa na Najeriya da suka hada da sojojin kasa da na sama da kuma 'yan sanda, sun dakatar da aiki a yankin Orlu na jihar Imo.
Yajin aikin da ‘yan kungiyar masu sana’ar tuka babur mai kafa uku da akafi sani da Adai-daita sahu ya gurgunta harkokin sufuri a birni da kewayen Kano.
A Senegal Fallou Diop kwarare mai sukuwar doki dan kasar da ya sharara a wasani kasa kuma mai shekaru 19 da haifuwa na shirin kara samun horo watanin uku a Faransa inda zai yi amfani da wani doki mai ruwa biyu- Senegal da kuma Faransa.
A Somaliya dakarun kasar suka bude wuta kan daruwan masu zanga zanga yayinda suke nuna damuwa kan jinkirin zabe. Har ila yau ba wata sanarwa akan wadanda suka mutu.
Domin Kari