Bayan da aka samu sassaucin hare haren ‘yan bindiga a yankin na Illela kwanakin baya sai gashi sun sake juyowa yankin tare daukar rayukan jama'a da dama.
Na tuntubi rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato akan wannan batun amma dai kakakin rundunar ASP Sanusi Abubakar yace bai samu tabbacin aukuwar lamarin ba a hukumance amma zai bincika, kuma zuwa hada wannan rahoton ban ji daga resa ba.
A Garin Gatawa na yankin Sabon Birni shima jama'a sun shiga halin kunci a kwanannan inda kauyuka fiye da hamsin suka yi hijira zuwa cikin gari.
Wakilin jama'ar a majalisar dokoki ta jihar Sakkwato Sa'idu Ibrahim Naino yace ko baya hijirar da jama'ar suka yi ‘yan bindigar basu kyale su ba.
A dayan bangaren kuma gwamnatin jihar Sakkwato ta kara tallafawa rundunar 'yan sanda da motoci kirar hilux guda 25 domin jami'an Puff ader rukuni na 2 domin su taimaka ga shawo kan matsalolin rashin tsaro a yankin na gabascin Sakkwato.
Su kuwa shugabannin al'ummar a yankin sun gabatar da wannan bukatar.
Ganin dai wannan ba shine karo na farko ba da gwamnati ke baiwa jami'an tsaro motoci abin jira yanzu ganin yadda wadannan zasu yi tasiri ko akasin haka da yake ayukkan ta’addancin ba ja baya suke yi ba.
Ga dai wani mazauni yankin Wanda ya shedi yadda aka kai harin: