Kasar Chadi ta yi kira na musanman ga kasashen duniya da su taimakawa kasashen yankunan Sahel biyar da kasar Faransa yayinda aka fara taro na musaman akan makomar shirinsu na yaki da ta'adanci.
Kungiyoyin mata a jamhuriyar Nijer suna kara neman hadin kan kasa yayinda ya rage kasa da mako 1 a gudanar da zabn shugaban kasa.
A Mali An saka hanu kan wata yarjeniyar wanzar da zaman lafiya kan rikicin Mali bayan wata ganawa a arewacin garin Kidal.
Annobar COVID 19 ta jefa ma’aikatan jinya da dama cikin yanayin da basu taba fuskanta ba. Kama daga fama da matukar gajiya, da fargaba, da bacin rai, da kuma nakasa. Wadannan kadan ne daga cikin yanayin da ma’aikatan jinya suka shiga sabili da annobar Korona da duniya ke fuskanta.
Ministar ayyukan jinkai ta Najeriya ta ce shirin kadamar da horon sa ido na zamantakewa zai taimakawa 'yan Najeriya kusan miliyan 13 a jihohi da dama.
Bazoum Mohamed yace sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki ya yi nuni da cewa jam’iyar PNDS da kawayenta na da rinjaye a sabuwar majalisar dokoki domin muna da kujeru 129 daga cikin kujerun wakilci 166
Jami’an tsaron kasar Somaliya 12 ne aka kashe, wasu 2 kuma suka raunata a jiya Lahadi, biyo bayan fashewar wani abu a gefen titi a tsakiyar jihar Galmudug, a cewar mahukunta
An gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin sojan Myanmar a rana ta uku a jere, yau Litinin, mako guda bayan da sojoji suka tsare Aung San Suu Kyi, da sauran shugabannin zababbiyar gwamnatin farar hula.
Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce ba zai dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Iran ba, har sai Tehran din ta rage yawan aikin bunkasa sanadarin Uranium din ta, kamar yadda aka cimma, a yarjejeniyar kasa-da-kasa ta 2015, wanda aka yi, don hanata hada makaman, na kare dagi.
Domin Kari