Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Tsaro Sun Dakatar Da Aiki A Yankin Orlu Na Jihar Imo


Biafra
Biafra

Dakarun sun kwashe kimanin mako guda suna fafatawa a wani yunkurin tarwatsa askarawan Eastern Security Network na kungiyar yan awaren Biafra ta IPOB da suka sansane a dazukan yankin.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, wani marubuci, Dakta Amanze Obi ya bayyana cewa "Sun ce sun dakatar, wannan na nufin cewa, suna iya dawowa a kowane lokaci. Ni kuwa ina mai ra'ayin cewa, kwatakwata ma bai kamata a gudanar da aikin ba. Saboda haka, dakatar da aikin ba shi muke roko ba. Abin da muke cewa shine a manta da aikin gaba daya saboda ba a bukatar gudanar da irin wannan aikin a wannan yankin. Kawai dai akwai bukata a shawarci askarawan Eastern Security Network kada su wuce gona da irin a yayin gudanar da aikinsu na kare dazukan yankin kudu maso gabas.

Al'ummar yankin sun ce abin da sauran al'ummar kasar suke yi a yankunansu ke nan. Kuma suna bukatar wata kungiyar tsaro da zata kare dazukan su a wannan yankin, tun da gwamnoninsu sun gaza,.

A nashi bayanin, Dakta Celestine Nwosu, wani malamin jami'a ya bayyana cewa, daidaita lamura a yankin Orlu bai fi karfin 'yan sanda da hukumomin leken asiri ba.

Bisa ga cewar shi, ba yaki ake yi a Orlu ba dake bukatar fatattaka daga kasa da sama, ko kuma mamayewa, saboda haka suna ganin daukar wannan matakin bai dace ba. Kuma dakatar da wannan aikin yana da kyau.

A hirar shi da Muryar Amurka, kakakin dakarun hadin gwiwar Laftanan Babatunde Zubairu ya bayyana cewa, "A halin yanzu an dakatar da wannan aikin. Ba wani bayani, an dakatar da aikin."

Saurari rohoton Alphonsus Okoroigwe cikin sauti:


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG