Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Gangamin 'Yan Hamayya Magoya Bayan Tsohon Shugaba Mahaman Ousman


Mahamane Ousmane
Mahamane Ousmane

A yayin taron gangamin da suka gudanar a cibiyar jam’iyyar RDR Canji, shugabannin jam’iyyun kawancen hamayya sun kara nanata watsi da sakamakon zaben 21 ga watan Fabrairun 2021 saboda a cewarsu jam’iyyar PNDS mai mulki ta yi satar kuri’u a garuruwa da dama musaman na jihar Tahoua.

Dan takarar zagayen farko na zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Fabrairu Habibou Kane Kadaoure na daga cikin shugabanin jam’iyyun adawa.

Jam’iyyun Kawancen CAP 20-21 da ACC da FRC sun nuna damuwa a game da matakin cafke wasu daga cikin abokan tafiyarsu wanda a cewarsu yunkuri ne na rufe bakin masu watsi da sakamakon zabe.

Shugaban jam’iyyar ORDN Tarmamuwa Maman Sani Adamou yace ba zasu aminta da kwace masu nasarar da dan takarar adawa Mahaman Ousman ya samu a zaben da ya gabata ba;

Da yake maida martani a dangane da korafe korafen na ‘yan adawa, kakakin jam’iyyar PNDS Assoumana Mahamadou na cewa a hadu a kotu don kawo karshen dukkan wani cece kuce mai nasaba da sakamakon zabe.

Shugaban Jam'iyyar PNDS Mohamed Bazoum
Shugaban Jam'iyyar PNDS Mohamed Bazoum

Matakin toshe yanar gizo gizon da hukumomi suka dauka tun a yammacin Talatar da ta gabata na daga cikin abubuwan da jam’iyyun hamayya suka yi tir da su a yayin wannan gangami da ke gudana a wani lokacin da ake shirin soma gurfanar da wasu jagororin adawa a gaban alkali bayan shafe awoyi 72 zuwa 96 a hannun ‘yan sandan farin kaya saboda zarginsu da hannu a tarzomar matasa masu watsi da sakamakon zaben 21 ga watan Fabrairu.

Wakilin Muryar Amurka a yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG