Tunji, ya kara da cewa “ba za su lamunci hakan na ci gaba da faruwa ba, kuma haka ne yasa za su gayyaci shugabannin 'ƴan kasuwan kasar, domin haɗa kai wajen lalubo maslahar da za ta kawo karshen tsawwala farashin kayayyaki da 'ƴan kasuwar ke yi, a wannan yanayi na matsin tattalin arziki da kasar ke fama dashi.”
Mr. Tunji, ya ce, “ba abin amincewa ba ne, a ga kungiyoyin 'ƴan kasuwa na sanya farashin da suka ga dama akan kayayyaki, don haka ya zama dole ga kowanne 'ɗan kasuwa ya makala farashin kayayyakinsa a bayyane.
Balarabe Tatari mataimakin shugaban 'ƴan kasuwa a jihar Kano, ya shaida cewa rashin bin diddigi da wannan hukuma ta yi, shine ya sa ta daura alhakin akan 'ƴan kasuwa.
Tatari, ya kara da cewa zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar ne yasa kamfanoni suka daina basu kaya, wanda hakan ne yasa kayayyakin suka yi ƙaranci a kasuwa, kuma hakan yasa wasu 'ƴan kasuwa suka yi amfani da wannan dama wajen kara farashin kayayyaki.
Dr. Isa Abdullahi Kashere malami kuma masanin tattalin arziki dake Jami’ar Kashere a jihar Gombe, ya ce “da ƙamshin gaskiya game da zargin da wannan hukuma ta yi ga 'ƴan kasuwa, domin a lokuta da dama 'ƴan kasuwa na fakewa da tsadar Dalar Amurka ko kuma janye tallafin Mai da Gwamnatin kasar ta yi, wajen tsawwala farashin kayayyaki domin cin kazamar riba.
'Ƴan Najeriya dai na ci gaba da bayyana koken su bisa hauhawar farashin kayayyaki a kasar babu ƙaƙƙauta wa.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5