Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Tarar Dala Miliyan 220, Hukumar FCCPC Ta Kuma Bukaci Kamfanin Meta Ya Kiyaye dokokin Najeriya


Meta
Meta

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cin kamfanin Meta tarar dala miliyan 220, inda ta ce binciken da ta gudanar ya gano an saba dokokin kare bayanai na kasar lokuta da  yawa a shafukan Facebook da WhatsApp.

A wata sanarwa da Hukumar kare hakkokin masu sayayya ta FCCPC ta fitar, ta lissafa hanyoyi biyar da kamfanin Meta ya saba dokokin bayanai a kasar da ke yammacin Afirka, ciki har da ta hanyar musayar bayanan ‘yan Najeriya ba tare da izininsu ba, nuna wariya da sauransu.

Nan take dai mai magana da yawun kamfanin Meta bai maida martini kan bukatar yin bayani a kan batun ba.

Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka, ta na da manyan rukunonin da aka fi amfani da intanet a duniya inda mutane miliyan 154 suka yi rijistar amfani da intanet a shekarar 2022, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.

Duk da yawan masu amfani da intanet a kasar, kamfanin Meta ya kasa bin dokokin kariyar bayanai ta Najeriya.

Bayan tarar dala miliyan 220, umurnin hukumar ya bukaci kamfanin Meta ya kiyaye dokokin cikin gida na Najeriya ya kuma daina “ci da gumin 'yan Najeriya masu amfani da shafukan.

A watan Mayun shekarar 2021 ne aka fara binciken saba ka’idodjin a lokacin da hukumar ta bude wani bincike kan wasu sabbin manufofin amfani da shafin WhatsApp. Ta kuma sanar da kamfanin Meta sakamakon binciken, lamarin da ya sa daga baya kamfanin ya gabatar da kudurin yin garambawul wanda ya kasa magance matsalolin farko, a cewar sanarwar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG