Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Sallami Shugabannin Hukumomin Gwamnati Biyu


FILE PHOTO: Nigeria's President Bola Tinubu looks on after his swearing-in ceremony in Abuja
FILE PHOTO: Nigeria's President Bola Tinubu looks on after his swearing-in ceremony in Abuja

Wadanda aka sallama sun hada da Babatunde Irukera, shugaban hukumar kula sahihancin ayuka da kayayyaki (FCCPC), da Alexander Okoh, shugaban hukumar kula da harkokin gwamnati (BPE).

WASHINGTON, D. C. - A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, shugaban kasa ya umurce su da su mika ragamar hukumomin ga manyan jami’ai na gaba, har sai an nada sabbin shugabanni.

A cewar sanarwar da aka fitar, wannan ya zo ne daidai da tsare-tsare na sake fasali da tsarin muhimman hukumomin gwamnatin tarayya, domin kare hakkin ‘yan Najeriya da kuma samar da wani kwakkwaran tubalin bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar manyan hukumomin samar da ci gaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG