Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnantin Tarayya Ta Rufe Katafaren Shagon Sahad Dake Abuja A Matakin Dakile Boye Kaya


Sahad Stores 1
Sahad Stores 1

Hukumar kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (FCCPC), ta rufe katafaren kantin Sahad Store, a unguwar Garki dake birnin Abuja.

WASHINGTON, D. C. - An dai zargi hukumar gudanarwar katafaren kantin da karin kudi akan wanda ke rubuce akan kayayyakin dake kan kanta.

Mataimakin shugaban riko na FCCPC Adamu Ahmed Abdullahi ne ya jagoranci samamen rufe kantin.

Da yake zantawa da manema labarai a yayin samamen, Abdullahi ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa hukumar gudanarwar kantin na ha’intar abokan cinikaiyya.

Ya kara da cewa shagon zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike.

Sahad Stores
Sahad Stores

“Abin da muka gano cewa wadannan mutane suna yi shi ne yaudarar farashi da rashin bayyana gaskiya a farashin, wanda ya saba wa sashe na 115 (3) na dokar da ta ce ba a bukatar mabukaci ya biya farashin wani kaya ko sabis mafi girma fiye da wanda yake rubuce a jikin kayan ba.”

“Sashi na 155 ya tanadi cewa duk wani kamfani da ya sabawa wannan doka, zai biya tarar Naira miliyan 100 ko ma fiye da haka kuma daraktocin kamfanin da kansu suna da alhakin biyan Naira miliyan 10 ga kowanne ko kuma daurin watanni shida a gidan kaso ko kuma duka biyun.

Sahad Stores
Sahad Stores

“Abunda muka aiwatar a yau shi ne mu tabbatar sun bi doka. Da farko mun kira su don su zo su kare kansu, amma ba su amsa kira ba. Daga baya sai suka aika da lauya wanda muka tambaye shi ko ya san gaskiyar lamarin. Sai Yace a’a

Sahad Stores
Sahad Stores

"Idan suna so a sake bude kantin, dole ne su tabbatar da cewa sun yi abin da doka ta buƙaci su yi."

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnonin jihohin kasar suka amince da kafa wani kwamiti da zai tunkari matsalar boye kayan masarufi a fadin kasar.

Gwamnantin Tarayya Ta Rufe Katafaren Shagon Sahad Dake Abuja A Matakin Dakile Boye Kaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG