WASHINGTON DC - A jiya Alhamis, Shugaban Rikon Hukumar FCCPC, Adamu Abdullahi, yayi cikakken bayani game da lamarin a shirin tashar talabijin ta Channels mai taken abuja a yau ko “dateline abuja” a turance.
A baya-bayan nan kamfanin Multichoice, wanda jigo ne a harkar yada shirye-shiryen talabijin ta kafar tauraron dan adam a yankin kudu da hamadar saharar Afrika kuma keda shelkwata a kasar Afrika ta Kudu, ya sanarda karin farashi akan ayyukan da yake gudanarwa a Najeriya, inda yace tsadar gudanar da harkokinsa a kasar ne ya wajabta karin.
A cewar kamfanin, karin farashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu mai kamawa.
Babban kunshin shirye-shiryen kamfanin dake kafar Dstv da a da ake biyan naira dubu 29 da 500 yanzu ya koma naira dubu 37, a yayin da karamin tsarin “compact plus” da ake biyan naira dubu 19 da 800 ya koma naira dubu 25.
Dandalin Mu Tattauna