A kwanan nan ne shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ziyarci babban birnin tarayya Abuja, bayan da ya gana da shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado ya zarce wajen shugaba mai jiran gado Janar Mohammad Buhari, don nanata cigaban hadin guywar kawo karshen kashe-kashe, da sace-sacen mata dake faruwa a arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaba Deby ya fadi cewa da yardar Allah Gamayyar kasashen biyu dake zaman membobin Tapkin Chadi, zata kawo karshen matsalar boko haram don samar da zaman lafiya mai dorewa. Kasashen biyu na fuskantar kalubale iri daya, inji shugaba Deby saboda haka ya zama wajibi suyi aiki tare don gano bakin zaren.
Janar Buhari yace Chadi, Camaru, da Niger na aiki tare da Najeriya don kawar da boko haram da raya tattalin arzikin yankin. Ya kuma kara da cewa da zarar ya karbi mulki za a sake irin wannan zaman don karfafa hadin guywa.
A bangaren ‘yan kungiyar PDP mai barin gado kuma, Masanin shari’a Abdullahi Jalo na goyon bayan fadada bincike akan masu hannu a kungiyar Boko haram da tamkar ake nuna kawaichi kan lamarin. Ya kuma yi kira ga Janar Buhari da yayi amfani da kotun masu aikata manayan laifuka ta duniya da ake kira ICC wajen bincike kamar yadda ta yiwa Isra’ila da Palasdinawa.
Chadi dai na da muhimmanci a wannan yakin da ake yi da ‘yan boko haram, don shugaba Deby ya taba cewa ya ma san maboyar Abubakar Shekau, madugun ‘yan kungiyar boko haram.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5