Rahotanni daga Jihar Kano nu nuni da cewa gwamnatin jihar ta dibi wasu yara kanana da ta kaisu makarantar marayu da ke jihar domin ilmantar da su da kuma basu kulawa ta musamman.
Daga cikin yaran akwai ‘yan shekaru hudu har zuwa 12 kamar yadda rahotanni ke nuna, sun kuma fito ne daga garuruwan Chibok da Baga da Damasak, bayan da suka rasa iyayensu sanadiyar hare-haren Boko Haram.
Wakiliyar Muryar Amurka, Baraka Bashir, ta ziyarci wadannan yara ta kuma zanta da su inda wasunsu suka gaya mata abinda suke so su zama a rayuwa a nan gaba.
“Ni dai a rayuwa inso na yi ilimi na taimaki al’uma” in ji daya daga cikin yaran, wanda kuma ya kara da cewa yana so ya zama shugaban kasa ne a nan gaba domin ya taimaki jama’a.
Shugaban makarantar marayun ta Kwankwasiyya, Malam Yahaya Salisu, ya ce har yanzu yaran ba su manta da abinda ya faru da su ba, ya kuma kara da cewa suna kokari su ga cewa sun taimaka musu wajen mantawa da lamarin.
“Yawancin da ya ke yara ne, har yanzu suna tunanin abin da ya same su, suna tunanin Boko Haram sun cucesu.” In ji Malam Salisu.
Gwamnatin jihar ta kano ta ce maksudin bude wannan makaranta shi ne domin a karkata hankulan yara kanana ga muhimmancin karatu.
“Ita harkar ilimi tana da lokaci, idan dan shekara shida ka bar shi ya kara wasu shekaru shida bai yi karatu ba to zai yi wuya ya yi karatu, shi ne muka ga ya dace duk cewa mu ma muna da matsaloli irin namu, muka dibi wasunsu domin a tallafa musu.” In ji gwamnan jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.