Wakilin Muryar Amurka Sanusi Lamido ya kara da cewa ko a baya bayan nan an samu kungigoyin kasa da kasa da suka gudanar da taruka na neman a soke zaben domin irin magudin da suka ce an tafka.
Sun kuma yi zargin cewa an tursasa mutane wajen yin zabe kana an razana wasu da dama ta hanyar harbe-harben bindiga a lokacin zaben.
Zaben na Jahar Rivers ana takaddama ne tsakanin dan takarar PDP Nyesom Wike da Dakuku Peterside na jam’iyar adawa ta APC.
A baya bayan nan ‘yan jam’iyyar ta APC suka gudanar da zanga zanga a ranar juma’ar da ta gabata a gaban ofishin hukumar zabe ta INEC bayan da hukumar zaben ta yi jinkiran bin umarnin kotu.
A kwanan ne kotun sauraren korafe-korafen zabe ta nemi hukumar at INEC da ta mika mata takardunzaben jihar.
A daya bangaren kuma, hukumar ta INEC ta ayyana cewa a ranar 23 na wannan wata za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jahar.
Ga karin bayani daga wakilinmu Sanusi Lamido a tattaunawarsu da Halima Djimrou: